Ambaliyar Ruwa: Arewa Ta Shirya Fuskantar Yunwa – Sarkin Zazzau

Mai marataba Sarkin Zazzau kuma uba ga hukumar da ke kula da kasuwar duniyar kasa da kasa ta Kaduna (KADCCIMA), Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yi kira ga arewa ta farka ta magance batun tsananin yunwa dake tunkarar yankin dalilin ambaliyar ruwa.

Da ya ke magana a taron KADCCIMA na bada lambar yabo na inganci karo na 3 a Kaduna, sarkin ya ce yankin ba ta bukatar dan duba ya fada mata cewa za ta fuskanci yunwa kuma akwai bukatar a farga domin noma ne abin da yankin ya dogara da shi.

“Batun yunwa yana tafe a bana, baka bukatar dan duba ya fada maka hakan, amma muna addu’a ga Allah da kuma wannan kiran cewa mutane su raba kafa domin idan ka tattare a wuri guda za ka sha mamaki. “Mu farka daga barcinmu mu ga abin da za mu iya yi kan tattalin arzikin mu wanda shine noma, musamman arewa.

Harkar noma ya fuskanci gagarumar matsala a bana saboda abu biyu, ambaliyar ruwa da kuma fitinar ‘yan bindiga.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply