Buhari Zai Ziyarci Koriya Ta Kudu Yau Lahadi

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tafi Koriya ta Kudu a ranar yau Lahadi don halartar taro kan harkokin lafiya na duniya da aka yi wa laƙabi da World Bio Summit, 2022.

Taron da gwamnatin Koriya da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) suka shirya, na kwana biyu ne da zai gudana tsakanin 25 da 26 ga watan Oktoba. Taken taron na bana shi ne ‘Makomar Rigakafi da Lafiyar Rai’ (‘The Future of Vaccine and Bio-Health).

A cewar sanarwar da Fadar Shugaban ƙasa ta fitar a ranar Asabar, an gayyaci Najeriya ne tare da wasu ƙasashen Afirka biyar game da ba da horo kan yadda za a dinga samar da rigakafin cutuka bisa fasahar mRNA a Afirka.

Mutane da dama ne za su yi wa Buhari rakiya zuwa taron, waɗanda suka haɗa da gwamnoni da ministoci da shugabannin ma’aikatu da sauran manyan jami’an gwamnati.

Ana sa ran Buhari zai koma gida bayan kammala taron, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Labarai Makamanta

Leave a Reply