2023: Ina Da Tabbacin Osinbajo Ne Shugaban Kasa – Sanata Gaya

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Sanata mai wakiltar Kano ta kudu, Sanata Kabiru Gaya, ya karɓi ragamar kungiyar cigaba (TPP), gamayyar kungiyoyin magoya baya masu yaɗa manufar mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Sanata Gaya, ya ce burin Osinbajo ba na ƙashin kansa bane, amsa kiran al’umma ne na tsayawa takara.

Sanatan ya ƙara da cewa ya na da kwarin guiwa Osinbajo ne zai gaji kujerar shugaba Buhari a zaɓen 2023, domin ɗorawa daga inda Buhari ya tsaya na ciyar da ƙasa gaba.

“Ba tare da wata tantama ba, ina da yaƙinin cewa duk wasu masu hankali anan sun fahimci tare da tabbatar da nagarta da cancantar Farfesa Yemi Osinbajo.” “Ta hanyar zaɓen mutum kamar Osinbajo, wanda ya san kalubalen da muke fuskanta fiye da tunani da kuma sanin dabaru da hanyoyin magance su, muna da babbar damar cigaba cikin ƙankanin lokaci.”

“Ina da kwarin guiwar cewa da karfin ikon Allah mai girma da ɗaukaka da kuma ruwan kuri’un miliyoyin ‘yan Najeriya a faɗin sassan ƙasar nan shida, Osinbajo ne zai gaji shugaba Buhari ranar 20 ga watan Mayu, 2023.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply