‘Yar’adua: Najeriya Ta Yi Rashin Shugaba Mara Kabilanci – Jonathan

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya bayyana tsohon maigidansa Umaru ‘Yar’adua a matsayin shugaba maras son zuciya.

Ya bayyana haka ne a wani ɓangare na ranar cika shekara 13 da rasuwar tsohon shugaban ƙasar na Najeriya.

Jonathan ya kasance mataimakin Umaru Musa Yar’Adua daga shekara ta 2007 zuwa 2010

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Juma’a, Jonathan ya rubuta cewa, “A wannan rana shekara 13 da ta wuce, ƙasarmu ta yi rashin gawurtaccen shugaba maras son zuciya, Shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua.

Mutum ne mai son zaman lafiya da adalci da kuma kamanta gaskiya.

“Muna waiwaye baya don nuna godiya ga Allah saboda rayuwarsa da kuma gudunmawar da ya bayar ga ƙasarmu.

“Shugaba Yar’Adua, jagora ne abin misali, wanda ya rayu ba tare da nuna bambancin ƙabilanci ko na addini ba. Kuma gudunmawarsa a fagen aikin gwamnati ta zaburas da mutane da yawa kan hanyar alheri.

“A yau, muna tuna shi da kuma hidimar da ya yi a rayuwarsa da jajircewa da duƙufa wajen tabbatar da dunƙulalliyar ƙasa daya mai bunƙasar arziƙi.

Goodluck Jonathan ya ce: “Za mu ci gaba da tunawa da shi saboda gagarumin ci gaban da ya kawo da kuma himmarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply