Mutunta Juna Shine Maganin Rikicin Manoma Da Makiyaya – Sarkin Fulani

A cigaba da daukan matakan ganin kawo karshen takaddama dake faruwa a tsakanin manoma da makiyaya an shawarci manoma da makiyaya da su kasance masu fahintar juna da kuma mutunta juna wanda hakan zai taimaka wajen samun zaman lafiya a tsakaninsu yadda ya kamata.

Sarkin fulanin Gundumar Masanawa dake karamar hukumar Kabo a jihar Kano kuma masanin Jimeta Yusuf Dan Umma ne ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Yola fadar gwamnatin jahar Adamawa.

Yusuf Dan Umma yace rikici da ake samu a tsakanin makiyaya da manoma ya kawowa harkokin noma da kiwo koma baya, don haka ya zama wajibi mutanen biyu suyi dukkanin abinda ya dace domin kaucewa faruwan rikici a tsakanin su.

Sarkin Fulanin ya kuma kirayi gwamnatin tarayya dana jihohi da suyi duk mai yiwa domin ganin an kai ga kawo karshen tashin hankali a tsanin makiyaya da manoma a fadin kasan nan musamman ma a wannan lokacin da ake girbe amfanin gona.

Dan Umma ya kuma kirayi manoma dama makiyaya da su daina daukan doka a hanunsu su kasance masu kaiwa hukuma karar abinda basu amince da su ba. Wanda hakan zai baiwa hukuma damar sasanta tsakanin su ba tare da wata matsala ba.

Ya kuma yi addua’r Allah madaukakin sarki ya taimaka wajen kawo karshen dukkanin kalubalen tsaro da ke ciwa Gwamnati dama al’umma tuwo a kwarya. Tare da shawartan ‘yan Najeriya da su cigaba da yin addu’o’i a koda yaushe domin ganin an samu damar kawo karshen matsalar baki daya.

Yusuf Dan Umma ya kuma shawarci matasa da suma su bada tasu gudumawar wajen gina kasa harma da wanzar da zaman lafiya a fadin Najeriya baki daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply