Kano: Shari’ar Rimin Gado Ta Dauki Sabon Salo

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewar Kotu ta bada umurnin tasa keyar tsohon shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Muhyi Magaji Rimin Gado, kurkuku ranar Juma’a, 29 ga Afrilu, 2022.

Wannan ya biyo bayan gurfanar da shi da gwamnatin jihar tayi a kotun majistare. A cewar Daily Nigerian, Muhyi ya bayyanawa kotu cewa bai da laifin zargin da ake masa na bada bayanin karya.

A karshe, Alkalin kotun, Aminu Gabari, ya bada belin Rimingado kan N500,000 da masu tsaya masa biyu.

Alkalin yace wajibi ne mutane biyun da zasu tsaya masa su kasance mahaifinsa da kawunsa kuma su gabatar da hujjar cewa sun biya haraji shekaru uku da suka gabata.

Labarai Makamanta

Leave a Reply