Harin ‘Yan Bindiga A Fadar Shugaban Kasa Ya Tabbatar Da Gazawar Buhari – PDP

Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana tsananin firgici da shiga tashin hankali game da fashin da ‘yan bindiga suka yi a kusa da fadar shugaban kasa, Aso Villa a babban birnin tarayya Abuja.

PDP ta nuna damuwa kan lamarin, tana mai zargin rashin iyawar shugaba Muhammadu Buhari ta fuskar bai wa kasar cikakken tsaro don kare rayukan al’umma, wanda wannan tabbas abin takaici da baƙin ciki ne.

A daren ranar Litinin ne fadar shugaban kasa ta fitar da wata sanarwa ta hannun mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu cewa ‘yan fashi sun afka gidan shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; lamarin da ya jawo cece-kuce.

A wata sanarwa da jam’iyyar PDP ta wallafa ta shafinta na Tuwita , ta ce: “PDP ta firgita da afkawar da ‘yan fashi da makami suka yi a fadar shugaban kasa ta Aso Villa, tana mai cewa hakan yana kara nuna rugujewar tsarin tsaro a karkashin kulawar Shugaba Buhari.”

Ta kuma bayyana matukar mamakin fashin duk da irin tsaro da ake bai wa fadar shugabanni a duk duniya. “A duk fadin duniya, Fadar Shugaban kasa, a matsayin matattarar iko da mulkin kasa take, ya zama wajibi ace ta samu tsaro yadda ya kamata tsaro mai ƙarfi.

“Saboda haka, duk wata matsalar rashin tsaro, musamman ta hanyar doka da oda, tana nuna wata alama ce mai hatsari ga tsaron kasar gaba daya.” “Jam’iyyarmu ta damu cewa idan har Shugaba Buhari ba zai iya tabbatar da tsaron fadar Shugaban kasa ba, to kuwa ba bu tabbacin ikonsa na bai wa kasar kariya.”

Karshe PDP ta yi kira ga shugaba Buhari da ya yi duba da tsarin tsaron kasar tare da tabbatar da daukar matakan da suka dace don inganta tsaro a fadin kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply