Halin Da Najeriya Ke Ciki Yanzu Abin Takaici Ne – Jonathan

Tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya koka kan karuwar aikata laifuka a kasar da yawaitar zubar da jini dake neman zama ruwan dare a Najeriya, yana mai cewa galibinsu shan miyagun kwayoyi ne ke jawo su.

Tsohon shugaban kasar ya kuma yi tir da bayyanar kungiyoyin asiri a makarantun sakandare da firamare A cewarsa, wannan ba karamin abin takaici bane saboda ya kara tabarbarewar yanayin tsaro a kasar, wanda ya dace a mike tsaye akai.

“Yanzu muna da kungiyoyin asiri a makarantun firamare da sakandare, a baya ya tsaya a manyan makarantu, amma yanzu zaku ga yara a wadannan makarantun suna tunanin yadda za su kashe sa’anninsu, wannan abin bakin ciki ne.”

Da yake halartar taro ta yanar gizo a ranar Juma’a, Jonathan ya kara da cewa matsalolin tabin hankali sun zama kalubale kasancewar mafi yawan ‘yan Najeriya suna cikin halin damuwa da abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma.

“Mafi yawan wadannan laifuffukan da aka tabbatar, shan kwayoyi ne suka haifar da su, saboda babu wani dan Najeriya mai hankali da zai je ya aikata laifi sai dai idan yana cikin mayen wani abu. “Ka yi tunanin farkawa da labarin kisan kai da safe, zai bar ka da tunani a zuciyar ka. Har ila yau, ya kamata mu kuma bincika batun lafiyar kwakwalwa.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply