Gombe: An Sanya Dokar Hana Zirga-Zirga A Ɓilliri

Gwamnatin jihar Gombe ta sa dokar hana fita ta awa 24 a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar saboda rikicin da ya ɓarke a garin na Billiri bisa naɗa sabon sarki.

A lokacin da yake magana da manema labarai ran Juma’a Sakataren gwamnati Farfesa Njodi ya ce an sa dokar ne don tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

Farfesa Njodi ya ce gwamnati a shirye take ta kare rayuka da dukiyoyi.

“Gwamnati ta dakatar da gudanar da duk wasu taruka a Billiri kuma an bai wa duka hukumomin tsaro umarnin tabbatar da an bi dokar,” a cewarsa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu mata da ƙananan yara daga garin Billiri da kauyuka masu makwabtaka sun tare hanyar Gombe da Yola tsawon kwanaki uku, suna zanga-zangar abin da suka ce gwamna Inuwa Yahaya ya ki naɗa sabon sarki wanda suke kira Mai Tangale.

Tare hanyar ya janyo cunkuson motoci da dama a hanyar ta Adamawa da Taraba da Benue da ma wasu jihohin ƙasar.

Mutanen yankin na Billiri na zargin gwamnan da son sanar da wani Dakta Musa Idris Maiyamba, wanda ba shi ne zabin mutanen ba.

Fusatattun Matasa sun bankawa Masallatai da sauran wuraren kasuwaci na musulmi wuta domin nuna ƙin amincewar su da naɗin sabon Sarkin garin wanda Musulmi ne.

Labarai Makamanta

Leave a Reply