Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Hukumar ya?i da cin hanci da rashawa (EFCC) ta maka alama kan wani gwamnan Arewa bisa zargin ya kwashi tsabar kudi biliyan N60 daga lalitar gwamnatin jiharsa ba bisa ka’ida ba.
Hukumar ta bayyana haka ne a wani sabon bayani da ta fitar ranar Lahadi 12 ga watan Disamba, 2021, kuma aka rarraba ga manema labarai a Abuja.
Sai dai EFCC tace gwamnan ya fito ne daga arewa maso tsakiya a Najeriya amma ba ta fa?i ainihin sunan shi ba, saboda wasu dalilai na tsaro.
Shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa, wanda yayi jawabi wajen wani taro, a birnin tarayya Abuja yace: “Ina mai shaida muku sabon sashin da muka kirkira na fasaha ya fara baiwa mara ?a kunya. Sun gano wasu bayanan sirri da dama.”
“?aya daga cikin abubuwan da muka gano shine wani gwamna daga cikin gwamnonin jihohin arewa ta tsakiya cikin shekaru shida da suka shu?e (mutum ?aya) ya zare tsabar kudi biliyan N60bn.” “Yanzun muna nazari kan lamarin ne, amma ina tabbatar muku da zaran mun kammala bincike zamu sanar da yan Najeriya aikin da muke ta bayan fage.”
Shugaban hukumar ya cigaba da cewa hukumarsa na aiki da wasu ma’aikatun gwamnati wajen amfani da fasaha a gudanar da aikinsu. “A siyasance mun gano wasu mutane kuma muna ha?a kai da wasu hukumomin gwamnati wajen tabbatar da mun bi matakan da ya dace wajen sa ido a harkokin gwamnati.”