Boko Haram: An Sallami Sojoji 700 Sakamakon Samun Naƙasa

Hukumar kula da mutane masu buƙata ta musamman ta Nijeriya NCPD, ta ce ta tallafa wa kimanin tsaffin sojoji 700 waɗanda aka sallama daga aiki saboda sun samu nakasa a lokacin da suke yaƙi da Boko Haram.

Babban Sakataren hukumar James Lalu ya bayyana haka a lokacin da ya bayyana gaban kwamitin Majalisar Dattawa kan ayyuka na musamman domin kare kasafin ma’aikatarsa na baɗi.

Lalu wanda ya ce akwai nakasassu a Nijeriya da yawansu ya kai miliyan 31.5 kuma adadin na daɗa ƙaruwa, ya buƙaci a ƙara yawan kuɗin da ake ware wa hukumar don su yi daidai da buƙatar ayyyukanta.

Ku kasance damu a shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun ingantattun ruhotanni da dumi dumin su

Labarai Makamanta

Leave a Reply