An Yi Nasarar Damke Mutumin Da Ya Yi Wa Tsohuwa ‘Yar Shekaru 85 Fyaɗe

Rundunar ‘yan sandan jihar Ekiti ta damke wani mutum mai suna Durodola Ogundele dake da shekaru 65 wanda ake zargi yayi wa matar mahaifinsa mai shekaru 85 fyade.

Kakakin rundunar Sunday Abutu ya ce ‘yan sandan kauyen Ido-Osi suka kamo Ogundele ranar Laraba.

Abutu ya ce kamar yadda labari ya iske su, shi dai Ogundele ya shiga dakin dattijiyar kuma matar mahaifinsa dake fama da ciwon kafa domin ya shafa mata magani a kafar. daga safa magani kuma sai ya aikata abinda ya so da karfin tsiya.

“Mun samu labarin cewa mahaifin Ogundele ya dade da rasuwar amma ita matar sa tunda ta tsufa sai ta ci gaba da zama a gidam mijin nata tare da ‘ya’yan sa.

Abutu ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar Tunde Mobayo ya bada umurin a kai file din Ogundele fannin gurfanar da masu aikata laifuka irin haka domin ci gaba da bincike.

Ya ce za a maka Ogundele kotu da zarar an kammala bincike akai.

Jihar Ekiti dai ta yi kaurin suna wajen samun mutane da ke bibiyar tsofaffi suna yin lalata da su da karfin tsiya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply