Albashi Zai Wadaci Ma’aikata Da Zarar Na Karbi Madafun Iko – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar zaɓaɓɓen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alwashin biyan ma’aikatan ƙasar albashin da zai ba su damar yin rayuwa ta mutunci da biyan buƙatun iyalansu.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na tuwita domin murnan Ranar ma’aikata ta duniya, Tinubu ya yi iƙirarin cewa zai haɗa hannu da ma’aikatan ƙasar domin a yaƙi talauci da rashin haɗin kai da banbance-banbancen addini a al’umma domin tabbatar da ci gaban Najeriya baki daya.

Ya yi bayanin cewa inganta rayuwan ma’aikata na ɗaya daga cikin muhimman alƙawuran da ya yi yayin da yake yaƙin neman zaɓe kuma ya bayar da tabbacin ɗaukar matakai domin ganin ya cika wannan alƙawari.

Tinubu ya nemi haɗin kan ɗaukacin ‘yan najeriya,domin a cewar sa dole ne a ɗauki tsauraran matakai domin a tabbatar ma’aikatan Najeriya sun sami ƙarin walwala.

Labarai Makamanta

Leave a Reply