Adam Zango Ya Kori Jaruma Ummi Rahab Daga Fim


Nan gaba kadan masu kallon shiri mai nisan zango na Farin wata za su ci karo da wata Sabuwar jaruma da aka maye gurbin Ummi Rahab da ita, bayan fitar da ita da maigidan na ta Adam A Zango ya yi daga cikin shirin.

Hakan dai ya biyo bayan takun sakar da suka samu wanda har ta kai ga sun yi rabuwar hannun riga, domin kuwa majiyar jaridar Dimokuradiyya ta tabbatar mana da cewar, Adam A Zango da Ummi Rahab, sun yi wata irin rabuwa ne ta Allah ya hada kowa da rabon sa, don haka ne ma Adamun ya Sha alwashin har abada ba zai Kara yin wani aiki da ita ba, hakan ne ma yasa, babu bata lokaci ya sauya ta da wata Sabuwar jarumar.

Duk wani kokarin da muka yi na samun Adam A Zango a waya , domin jin abin da ya faru daga gare shi har zuwa lokacin da muka hada wannan labarin ya ci tura, ya yin da ita ma Ummi Rahab mun yi ta kiran wayar ta a kashe.

Amma dai majiya mai karfi da ta ke kusa da Adamun ta tabbatar mana da faruwar lamarin. Kamar yadda wani na kusa da shi Adam A Zango ya bayyana mana cewar, ba wannan ba ne karo na farko da hakan ta ke faruwa tsakanin shi Adamu da jarumai mata, domin ko a shekarun baya irin wannan ta taba faruwa tsakanin sa da Rahama Sadau, wanda kuma daga baya suka shirya.

Yanzu dai abin jira a gani shi ne, ko cire Ummi Rahab daga cikin fim din Farin wata, zai taba labarin fim din ko a’a?

Labarai Makamanta

Leave a Reply