2023: Haramun Ne Jonathan Ya Tsaya Takara – Falana

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar fitaccen lauya kuma ɗan gwagwarmaya, Femi Falana ya bayyana cewa tsohon Shugaban Ƙasa Goodluck Jonathan ba zai yiwu ya sake shugabancin Najeriya ba har abada.

Falana ya ce babu yadda za a yi Jonathan ya ma tsaya takara a zaɓen 2023, ballantana har ya sake zama shugaban ƙasa.

Falana ya ce kundin dokokin Najeriya ya haramta wa tsohon shugaban sake tsayawa takara ballantana kuma a sake rantsar da shi kan mulki.

Lauyan ya yi wannan kakkausan gargaɗin da ƙarin haske ne a ranar Laraba, daidai lokacin da ake ta kiraye-kirayen Jonathan ya gaggauta sauya sheƙa zuwa APC domin a tsayar da shi takara.

Falana ya ce idan Jonathan ya sake fitowa takara, to ai ya karya dokar Najeriya wadda ta ce iyakar zango biyu kaɗai shugaban da aka zaɓa zai yi a dokance.

Jonathan kuwa an rantsar da shi a cikin 2010, inda ya ƙarasa zangon marigayi Umaru ‘Yar’Adua, kuma an rantsar da shi cikin 2011, lokacin da ya lashe zaɓen 2011.

Falana ya ce idan Jonathan ya sake tsayawa takara, to idan ya ci zai kasance shekaru 9 zai yi kenan kan mulki, maimakon adadin shekaru 8 kacal na zango biyu da kundin tsarin mulkin Najeriya ya gindaya.

“Doka ya soke takarar shugaban ƙasa ta 2023 da aka ta raɗe-raɗi kan Jonathan. Domin tunda ya yi shekara ɗaya ta sauran mulkin Yar’Adua, ai kenan zai yi shekaru 9 ka mulki kenan. Wannan kuwa ya saɓa da Sashe na 137 na Kundin Dokokin Najeriya, wanda ya ce shugaban ƙasa zango biyu kaɗai zai yi na tsawon shekaru biyu.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply