Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Mun Cire Sama Da Mutum Miliyan 100 Daga Talauci – Ministar Jin Kai

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnatin Tarayya ta ce ta kashe naira biliyan 35.5 kan shirye-shiryen taimakawa al’umma a Jihar Taraba tun lokacin da ta ci mulki.

Ministar Jin-ƙai da kare Afkuwar Bala’i ta Najeriya Hajiya Sadiya Farouq ce ta bayyana haka a Jalingo babban birnin jihar, yayin da take wata tattaunawa da waɗanda suka ci moriyar shirye-shiryen.

Ministar wadda shugabar shirin a jihar Beatrice Kitchina ta wakilta ta ce mutum sama da miliyan 100 sun fita daga cikin matsanancin talauci dalilin wannan shiri, kuma ciki har da matasa da mata.

Ta bayyana jerin wasu shirye-shirye kamar su N-Power da CCT da GEEP ga kuma shirin ciyar da ‘yan makaranta shi ma.

Sakataren shirin ciyar da ‘yan makarantar Idris Goje, yace an yi maganin talauci a ƙasa da wannan shiri, haka kuma ya yi amfani a jihar Taraba.

Exit mobile version