Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Mun Fidda Sama Da Mutum Miliyan 10 Daga Talauci – Ministar Jin Kai

Gwamnatin Buhari ta lashi takobin fidda yan Najeriya milyan 100 daga cikin talauci nan da 2030

Ministar tattalin annoba da tallafi, Sadiya Farouq, ta bayyana adadin da aka fiddar kawo yanzu

A cewarta, an rage hanya tun da an fitar da mutum milyan 10 cikin shekaru 6

Gwamnatin tarayya ta fidda sama da yan Najeriya milyan 10 daga cikin bakin talauci ta shirye-shiryen tallafi da jin kai ta NSIP, cewar Minista Sadiya Farouq.

Hajiya Sadiya Umar Farouq, wacce take rike da kujerar Ministar tattalin annoba da tallafi, ta sanar da hakan ne a taron lissafin adadin mutanen dake fama da talauci a kasashe masu tasowa.

A jawabin da mai magana da yawunta, Nneka Ikem Anibeze, ya fitar ya bayyana cewa: “Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta samu nasarar karfafa mutum sama da milyan goma da kuma tsamosu daga talauci ta shirye-shiryen gwamnatin masu yawa, wanda ya hada da shirin tallafi na NSIP.

An yi wadannan abubuwa ne saboda adadin yan Najeriya ya kai milyan 200.” Farouq ta kara da cewa gwamnatin tarayya zata hada kai da kamfanoni masu zaman kansu domin bibiyan mutanen dake fama da talauci don taimaka musu da kuma tsamosu daga ciki.

Ta godewa bankin duniya, UNICEF, da kuma kungiyoyin tallafi bisa gudunmuwan da suke badawa wajen ganin an yakice talauci a duniya nan da 2030.

Exit mobile version