An Nada Shugaban Asusun Ba Wa Dalibai Bashin Kudin Karatu

IMG 20240427 WA0072

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Jim Ovia, CFR a matsayin shugaban asusun bai wa ɗalibai bashin karatu. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce yana da yaƙinin mista Ovia zai yi amfani da ƙwarewarsa ta aiki wajen ganin ɗaliban ƙasar sun samu damar faɗaɗa karatu ta hanyar samun bashi daga shirin da gwamnatinsa ta ɓullo da shi. Mista Ovia – wanda fitaccen ma’aikacin banki ne, kuma ɗan kasuwa – na da digiri na biyu a fannin…

Cigaba Da Karantawa

Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Bada Tallafin Karatu Ga Daliban Arewa

Gidauniyar tunawa da marigayi Sardaunan Sokoto Sir Ahmadu Bello ta ba da tallafin karatu ga dalibai 200 wadanda suka fito daga jihohi 19 na Arewa har da Abuja. Shugaban Gidauniyar Injiniya Abubakar Gambo Umar ya sanar da hakan a tattaunawar shi da manema labarai jim kaɗan bayan kammala bikin bayar da tallafin wanda ya gudana a Kaduna. Injiniya Gambo ya ƙara da cewar tallafin karatun kebe shi ne kawai ga dalibai dake karantar ɓangaren kimiyya da fasaha a manyan makarantun Najeriya. “Mun zaɓo dalibai guda goma goma daga jihohi 19…

Cigaba Da Karantawa

Ilimin ‘Ya’ya Mata Shi Ne Tubalin Ginin Al’umma – Alawiyyah Aminu Dantata

An bayyana ilimin ‘ya’ya Mata a matsayin wani tubali wanda ke gina al’umma gaba daya kasancewar duk wanda ya ba ‘ya mace ilimi to tamkar ya ba al’umma gaba daya ne. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar makarantar Nurul Huda Islamic Academy dake Kaduna Hajiya Alawiyyah Aminu Dantata lokacin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala bikin yayen daliban makarantar wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna. Ta ƙara da cewar a tsarin da suka ɗauka a makarantar Nurul Huda shine bada…

Cigaba Da Karantawa

Ilimin ‘Ya’ya Mata Shi Ne Tubalin Ginin Al’umma – Alawiyyah Aminu Dantata

An bayyana ilimin ‘ya’ya Mata a matsayin wani tubali wanda ke gina al’umma gaba daya kasancewar duk wanda ya ba ‘ya mace ilimi to tamkar ya ba al’umma gaba daya ne. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Shugabar makarantar Nurul Huda Islamic Academy dake Kaduna Hajiya Alawiyyah Aminu Dantata lokacin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala bikin yayen daliban makarantar wanda ya gudana a gidan tarihi na Arewa dake Kaduna. Ta ƙara da cewar a tsarin da suka ɗauka a makarantar Nurul Huda shine bada…

Cigaba Da Karantawa

Babban Gata Da Za A Yi Wa Yara Shi Ne Ba Su Ilimi – Ambasada Musawa

An bayyana cewa babban gata da iyaye za su yi wa ‘ya’yan su shine basu ingantaccen ilimi na addini da na zamani wanda hakan zai sa su zama abin alfahari ga ƙasa nan gaba. Da yake zantawa da manema labarai a Kaduna a yayin bikin yaye daliban makarantar Nurul Huda da ya gudana a Arewa House Kaduna, Ambasada Dr Ismail Musawa ya ce ilimi bai da tsada ko da nawa za a kashe wajen neman shi. Dr Musawa ya ƙara da cewa ilimi shi ne tsani guda da ya rage…

Cigaba Da Karantawa

ASUU Ta Bukaci A Sauya Shirin Bashin Karatun Dalibai Zuwa Tallafin Karatu

Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar ba da bashin karatu ga dalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin bai wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi mai zurfi. A wata hira da gidan Talbijin na Channels ranar Lahadi, shugaban ASUU ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwuwa ba. A cewarsa, bayar da bashi don yin karatu “ba zai dore ba”. Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, “tunanin bayar da bashin karatu ga dalibai ya zo ne a…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Daidai Da Ta Hana Malaman Jami’a Albashi – Kotu

Kotun kwadago ta Najeriya ta zartar da hukuncin cewa matakin da gwamnatin kasar ta dauka kan kungiyar Malaman Jami’a na kin biyan mambobinta da suka shiga yajin aiki albashi yana kan doka. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Shugaban kotun mai shari’a Benedict Kanyip, ne ya bayyana hakan yayin da yake sanar da hukuncin, inda ya ce gwamnatin tarayyar tana da ikon rike albashin ma’aikatan da suka shiga yajin aiki. Sai dai kuma a bangaren tsarin biyan albashi kotun ta zartar da cewa, ya saba wa tsarin ƴancin cin gashin…

Cigaba Da Karantawa

Zulum Ya Bukaci A Janye Karin Kudin Makaranta Da Aka Yi A Jami’ar Maiduguri

Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno ya yi kira ga shugabannin jami’ar Maiduguri da ke jihar da su janye sabon karin kudin karatu da suka yi. Rahoton ya nuna Mai girma Babagana Umara Zulum ya yi wannan kira ne domin a tausayawa marasa karfi da ke karatu. Sannan Farfesa Babagana Zulum yana ganin idan aka rage kudin makarantar, hakan zai saukakawa wadanda rikicin yakin Boko Haram ya auka masu. Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin da wasu daga cikin shugabannin jami’o’in jihar suka kai masa ziyarar sallah a…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Kammala Rijistar Sabuwar Kungiyar Malaman Jami’a

Gwamnatin tarayyar ta kammala yi wa sabuwar ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasar mai suna ‘Congress of University Academics’ (CONUA). Ministan ƙwadago na ƙasar Dakta Chris Ngige, ne ya bayyana haka ga manema labarai jim ƙadan bayan tattaunawar sirri da shugabannin sabuwar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin shugabanta Niyi sunmonu. Ministan ya kuma gargaɗi sabuwar ƙungiyar da cewa kada ta ɗauki hanyar da takwararta ta ‘Academic Staff Union of Universities’ (ASUU). ta bi Ya umarci ƙungiyar da ta yi aiki a duka jami’o’in ƙasar ba tare da fargabar kowa ba, yana mai cewa…

Cigaba Da Karantawa

Babu Wani Cigaba Da Gwamnatin Buhari Ta Samu – Bishop Kukah

Labarin da muke samu daga Jíhar Sokoto na bayyana cewar Babban Bishop na Cocin Sokoto Bishop Matthew Hassan-Kukah ya ce duk da irin manyan alkawura da dama da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi, a yanzu zai bar ‘yan Najeriya “a matsanancin talauci” fiye da lokacin da ya amshi mulki a 29 ga watan Mayu, 2015. Fitaccen malamin addinin ya kara da cewa baya ko tantama lafiyar Buhari ta karu a tsawon shekaru bakwai da rabi da suka shude amma yaso a ce miliyoyin ‘yan Najeriya sun mori tagomashi daga ingantacciyar…

Cigaba Da Karantawa

Katsina: Masari Ya Sallami Shugaban Jami’ar Umaru Yar’adua

Labarin dake shigo mana daga jihar Katsina na bayyana cewar Majalisar Zartaswa Jihar Wadda Gwamna Aminu Bello Masari ke Jagoranta ta Amince da Shugaban Jami’ar Umaru Musa Yar’adua dake Katsina Farfesa Sanusi Mamman ya gaggauta Ajiye muƙaminsa, Sauke shi daga muƙamin ya biyo bayan Rahotan da Gwamna ya kafa ne ya ba shi shawara, kan Rahotan da aka gabatar mashi akan Korafe-korafe da aka gabatar akansa. Mai baiwa Gwamna Shawara kan Ilimi mai Zurfi, Dakta Bashir Usman Ruwan Godiya ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da maanema…

Cigaba Da Karantawa

An Amince Da Koyar Da Yara Karatu Da Harsunan Gida A Makarantu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Majalisar ministoci ta amince da wata manufa kan amfani da harsunan gida wajen koyar da dukkan daliban kasar a matakin firamare a fadin kasar. Ministan Ilimi Adamu Adamu ne ya sanar da haka  ga manema labarai, bayan taron majalisar ministoci da aka yi a ranar Laraba cewa majalisar ta amince a aiwatar da sabon tsarin amfani da harsunan gida da ake kira National Language Policy wanda ma’aikatarsa ta kirkiro. Ministan ya bayyana cewa ” ka’idojin koyarwa na shekaru shida na farko a…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Dawo Da Darasin Tarihi A Makarantu

Gwamnatin tarayya ta sanar da dawo da darasin tarihi a matsayin darasi mai zaman kansa a cikin manhajar ilimi na matakin farko a Nijeriya, shekaru 13 bayan an soke shi. Ministan Ilimi, Adamu Adamu ne ya bayyana hakan a yau Alhamis a Abuja, wajen bikin kaddamar da shirin sake koyar da ilimin tarihi da horar da malaman tarihi a matakin farko. Ya nuna damuwar sa da yadda hadin kai a Nijeriya ya yi ƙaranci, inda mutane su ka saka kabilanci a zuƙatansu, inda ya ƙara da cewa rashin samun ilimin…

Cigaba Da Karantawa

Rabin Albashi: ASUU Ta Yi Barazanar Sake Tsunduma Yajin Aiki

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ta yi wata kwarya-kwaryar zanga-zanga kan rikicinta da gwamnatin tarayya da kuma rashin biyansu cikakken albashi a watan da ya gabata. ASUU ta ce wannan zanga-zanga sun yi ta ne don nuna damuwa ga yadda ake yiwa Malaman rikon sakainar kashi da kuma alanta tsarin ‘ba aiki ba albashi a kansu’, da kuma tursasa su su koma bakin aiki ba tare da samun hakkinsu ba. Kungiyar ta ce, matukar gwamnati ta gaza biya musu bukata,…

Cigaba Da Karantawa

Sulhu Ya Kamaci ASUU Ba Yajin Aiki Ba – Shugaban Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shawarci kungiyar malaman jami’o’i da sauran kungiyoyin ma’aikata da su rungumi sulhu da gwamnati tare da gudun yajin aiki a matsayin hanyar neman a biya musu bukatu. Buhari ya bayyana hakan ne a taro na 74 na yaye dalibai a jami’ar Ibadan a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba shekarar da muke ciki ta 2022. Shugaba Buhari ya samu wakilcin farfesa Abubakar Rasheed ne a taron, wanda shine babban sakataren hukumar jami’o’i ta kasa (NUC). Buhari ya kuma yaba da kokarin gudunarwar jami’ar Ibadan bisa…

Cigaba Da Karantawa

Ba Za Mu Biya ASUU Albashin Aikin Da Basu Yi Ba – Ministan Ilimi

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar yayin da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ke gudanar da zanga-zangar lumana a faɗin jami’o’in ƙasar domin nuna rashin jin daɗinsu game da rashin biyansu albashin watannin da suka kwashe suna yajin aiki, gwamnatin tarayya ta ce ba za ta biya malaman albashin aikin da ba su yi ba. Ministan ilimin Malam Adamu Adamu ne ya bayyana haka ranar Laraba bayan taron majalisar zartarwa da shugaban ƙasar ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar da ke Abuja babban birnin ƙasar. Yayin da…

Cigaba Da Karantawa

Rikicin ASUU: Ya Zama Tilas Buhari Ya Biya Albashin Su – Falana

Fitaccen lauyan nan mai rajin kare hakkin dan adam a Najeriya Femi Falana (SAN) ya shawarci shugaban ƙasar Muhammadu Buhari da ya bayar da umarni a biya malaman jami’o’in ƙasar duka albashinsu na wata takwas. Wasu daga cikin malaman Jami’o’in ne dai suka yi ƙorafin cewa an biya su rabin albashinsu a watan Oktoba, maimakon albashin wata takwas da suka yi alkawari da gwamnati gabanin janye yajin aikin. To sai a martanin da gwamnatin tarayyar ta yi ta ce ba zai yiwu a biya malaman albasahin aikin da ba su…

Cigaba Da Karantawa

Da Yiwuwar ASUU Ta Sake Tsunduma Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU na shirin sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta na biya musu bukatunsu. A wata tattaunawa da mataimakin shugaban kungiyar da BBC ta yi, Dr Chris Piwuna, ya ce kungiyar na shirin gudanar da taron gaggawa domin yanke shawara a kan matakin da za ta dauka a cikin kwanakin nan. ‘’Za mu hadu nan gaba mambobinmu suna mana tambayoyi dole mu hadu mu san amsar da za mu ba su,’’ in ji shi. Malaman na korafi kan yadda…

Cigaba Da Karantawa

Gwamnatin Tarayya Ta Biya ASUU Albashin Rabin Wata

Gwamnatin tarayya ta biya Malaman jami’a dake karkashin kungiyar malamai masu koyarwa ta ASUU albashin kwanaki 18 na watan Oktoba, domin rage musu radadin rashin albashi na tsawon watanni takwas da suka shafe suna yajin aiki. Malaman jami’o’i da dama da Wakilinmu ya tuntuba sun tabbatar da hakan inda suka ce an biya su rabin albashinsu ne kuma yana nuna na watan Oktoba ne. A bayanin da wani malamin jami’a yayi wa wakilinmu yace ya samu albashin babu zato balle tsammani duk da cewa ba wannan bace yarjejeniyar dake tsakaninsu…

Cigaba Da Karantawa

Hukumar Yaki Da Rashawa Ta Kulle Jami’o’i 62 Na Bogi

Hukumar da ke yaki da almundahana da sauran lafukan da suka shafi cin hanci ta ICPC ta ce ta rufe jami’o’i da kwalejin kimiyya da fasaha da ke bayar da shaidar digiri na bogi 62 a fadin kasar. Hukumar ta ce wannan abu ne da ke neman zama ruwan dare a Najeriya, domin kuwa babu wata jiha a fadin kasar da ba a samu irin wannan makarantu ba a cikinta. Cikin shekaru da ICPC ta kwashe tana gudanar da wani bincike a boye, ta kai ga gano adadin makarantu da…

Cigaba Da Karantawa