Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Za Mu Hada Hannu Da Tìnubu Wajen Inganta Rayuwar ‘Yan Najeriya – Gwamnoni

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce inganta rayuwar ‘yan Najeriya ne babban abin da gwamnatinsa ta fi baiwa muhimmanci.

A cewar Daraktan yada labarai na fadar shugaban kasa, Abiodun Oladunjoye, shugaban kasar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin mambobin kungiyar gwamnonin APC karkashin jagorancin gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar gwamnati.

Rahotanni sun ce shugaban ya ce gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi za su yi aiki tare a kan mafi karancin albashi, wanda abu ne da ya ce ya kamata a duba.

Tinubu ya bukaci gwamnonin da su yi amfani da damar da miliyoyin ‘yan kasa suka ba su domin kawo sauyi a rayuwar jama’a. Ya kuma kara da cewa zai yi aiki don jin dadin ‘yan Najeriya.

“Wannan taron ba bakon abu bane a gare ni, kuma abubuwan da taron ya kunsa na da matukar muhimmanci. Hadin kan na da ban sha’awa sosai. Wannan ya shafi aikin Najeriya ne ba Bola Tinubu ba,’’ in ji shi.

Shugaban ya ce za a daidaita farashin canjin dala, a inda yake cewa gwamnati abu ne mai ci gaba.

“Na gaji kadarori da kuma basussukan wanda ya gabace ni. Wannan shi ne karon farko da kuka shiga zauren majalisar, kuma wannan ne karo na farko da zan yi taro“.

Tinubu ya bayyana farin cikinsa da ganin cewa jam’iyyar APC ke da rinjaye a Majalisar dokoki ta kasa da na wasu jihohi, wanda hakan zai sa a samu sauki wajen samar da manufofin da za su shafi tattalin arziki da jama’a kai tsaye.

A nasa jawabin mataimakin shugaban kasa, Sen. Kashim Shettima, ya yi kira ga gwamnonin da su bai wa shugaban kasa hadin kai yayin da yake tunkarar kalubalen da ke durkusar da tattalin arzikin kasar, kamar tallafin man fetur da kuma farashin canji da ake da su daban-daban..

Exit mobile version