Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Cire Tallafin Mai: Za A Raba Wa ‘Yan Najeriya Biliyan 500 Domin Rage Radadi – Tinubu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yace yana sane da halin da ‘yan Najeriya ke ciki na wahala sakamakon matakin da ya dauka na cire tallafin man fetur, sai dai yace an dauki matakin ne saboda shi ne mafi inganci ga kasar da kuma kare makomar ta.

Tinubu yace wannan ne dalilin da ya sa ya bukaci Majalisun kasar da su amince masa da kasafn kudin naira biliyan 500 domin sanya su ta hanyoyin da zasu ragewa talakawa radadin cire tallafin. 

Shugaban yace yanzu haka gwamnatin sa na ta kokarin tsara dabarun da za tayi amfani da su wajen tallafawa jama’a, a dai-dai lokacin da suke inganta hanyoyin da za’a bi wajen ganin tallafin sun kai ga wadanda ake yi domin su. 

Tinubu yace baya son ganin shirin nan na aikewa talakawa kudade ya samu targade ta inda za’a dinga aikewa wadanda bai kamata su ci gajiyar shirin ba, yayin da ya bayyana fatar ganin sabon shirin ya samu nasara. 

Shugaban ya bayyana wannan shiri ne lokacin da ya karbi tawagar tsoffin gwamnonin da suka yi aiki da shi tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007 lokacin da ya jagoranci gwamnatin jihar Lagos. 

Tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion ya jagoranci tsoffin gwamnonin 16 zuwa fadar shugaban kasar dake Abuja domin taya Tinubu murnar nasarar da ya samu na zama shugaban Najeriya. 

Exit mobile version