Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kotu Ta Tura Tsohon Ministan Lantarki Kurkuku

Tsohon karamin ministan wutar lantarki na Najeriya, Muhammad Wakil, zai zauna a gidan yari har zuwa ranar 31 ga watan Maris 2021 bisa umarnin babbar kotun tarayya dake Abuja.

Ana zargin Wakil da almundahanar kudade har biliyan N27 wanda aka ware domin biyan tsoffin ma’aikatan NEPA hakkinsu na murabus.

Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ce ta gurfanar da Wakil a ranar Litinin a kan zarginsa da ake yi da laifuka biyu, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.

An gurfanar da tsohon dan majalisa Wakil tare da wasu kamfanoni biyu, Corozzeria Nigeria Limited da Pikat Properties Nigeria Limited, a kan zarginsu da ake yi da karbar N148 miliyan dagac Bestworth Insurance Brokers Limited daga ikin N27.1 biliyan wanda kamfanin inshora ta amince a fitar musu.

Exit mobile version