Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon ministan sufurin jiragen saman Najeriya, a zamain mulkin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika da yarsa Fatima kan naira miliyan 100 kowannen su.
A ran Alhamis ne aka gurfanar da Sirika da ?arsa a gaban kotun.
Hukumar EFCC ce ta maka tsohon ministan a kotu domin a kwato wasu Naira biliyan 2.7 da take zargin an tafka harkalla a kansu lokacin yana minista.
Sirika ya yi shekara takwas ya na Ministan sufuri sannan an gurfanar da shi tare da yarsa Fatima, sai Jalal Hamma da kuma kamfanin Al-Duraq Investment Limited, bisa tuhumomi shida a kan su.
Ana neman Naira biliyan 2.7 a hannun su.
Tun a ranar 23 ga Afrilu Hadi Sirika yake tsare a hannun EFCC a Abuja, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito.
An tsare shi a Ofishin Shiyya na EFCC da ke kan titin Formella Street, Wuse 2 Zonal Office.
Zaman kotu
Masu bincike sun gayyaci tsohon ministan domin yi masa tambayoyi, dangane da wata kwangila da ake zargin an dan?ara zambar ma?udan ku?a?e a cikin ta, wadda aka yi a Maaikatar Harkokin Sufurin Jiragen Sama a zamanin sa.
Tun a lokacin ya amsa gayyata, kuma aka tsare shi. Haka wata majiya daga EFCC ta shaida.
A zamanin Hadi Sirika ne ya na minista ya ?addamar da Jirgin Najeriya, wanda daga bisani aka gane abin ashe duk gidoga ce da rufa-rufa.
Mai sharia Sylvanus Orji ya amince da bukatar belin wadanda ake tuhumar, bayan sun ki amsa tuhume-tuhumen da ake yi musu.
Bayan sauraron dukkan bangarorin, Mai sharia Orji ya bayar da belin kowanne daga cikin wadanda ake tuhuma a kan kudi miliyan 100 tare da tsayayyu biyu kowanne.
Mai sharia Orji ya kara da cewa rashin cika sharuddan belin zai sa a tura wadanda ake tuhuma zaman gidan gyaran hali.
Dole ne daya daga cikin wadanda za su tsaya ma wanda aka beli ya kasance yana da kadarar a cikin Babban Birnin Tarayya.
Sannan kuma wadanda ake tuhumar kada su yi balaguro zuwa wajen kasar.
Daga ?arshe sai aka garga?i wa?anda ake tuhuma cewa duk wanda ya kasa cika sharuddan belin, za a tsare shi a gidan gyara halin.
Za a ci gaba da shariar a ranakun 10, 11 da 20 ga watan Yuni.