Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Kashe-Kashe A Arewa: ‘Yan Kishin Kasa Sun Bukaci A Tsige Buhari

Kiran Gaggawa Ga ‘Yan Majalisar Nijeriya Na Arewa Da Su Gaggauta Tsige Shugaba Buhari Muddin Ya Ki Sauya Hafsoshin Tsaro

  1. Da alama dai jinin mutum dari da goma da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi wa yankan Rago yana neman tafiya a banza, yau fiye da mako guda da faruwar wannan lamari amma babu wata tsiya da muka ga gwamnatin Najeriya ta tsinana wajen daukarwa wadannan manoma fansa ba kuma mu ga anyi wata hobbasa wajen kakkabe ‘yan ta’addan ba.
  2. Duk da zaman tattaunawa da shugaban kasa yayi da hafsoshin tsaro tare da shelanta farmakin mutuwar kare dangi da shugaban yayi a kan ‘yan ta’addan, kawo yanzu ba mu ga komai game da ikrarin shugaban ba, dama anyi irin wannan zama yafi a lissafa, amma babu wani abu da ke canzawa.
  3. Har kawo yanzu babu wani kokari da shugaban kasa ke yi wajen magance matsalar tsaron da ta addabi arewacin kasar nan, duk da kiran da majalisar dattawa tayi na sauke hafsoshin tsaro. Babu wata alama da ke nuna shugaban zai canza wadannan mutane. Kenan a haka za a cigaba da tafiya ana salwantar da rayukan ‘yan kasa marasa laifi ana kama mata ana musu fyade? Lallai ya kamata majalisa ta gaggauta ceto al’ummar kasar nan ta hanyar tsige Buhari.
  4. Na ji wasu na cewa wai tsoron juyin mulki ya hana Buhari sauya wadannan hafsoshi wadanda gazawarsu ta bayyana a zahiri. Idan haka ne kenan Buhari ya zabi ya fifita mulkinsa a kan dubban rayukan al’umma da ake salwantarwa, ya gwammace ya cigaba da mulki ‘yan ta’adda su cigaba da zubar da jinin bayin Allah. Idan haka ne don Allah akwai burbushin tausayi da mutuntaka a tattare da wannan mutumi? Idan da Shugabanmu nagari ne kamar yadda masoyansa ke ikrari, kamata yayi ya sauka yayi murabus ba sai an fara maganar juyin mulki ba, tunda ya gaza kiyaye rayukan al’umma, mutuncinsu da dukiyarsu.
  5. Shugaba Buhari ya kassara tattalin arzikin Najeriya ya jefa shi cikin mummunan yanayi, ya kuma karbo bashi na tiriliyoyin kudade wanda hakan ya kawo babban nakasu da koma baya ga kasarmu uwa Najeriya.
  6. Al’ummar Najeriya ta sami kanta cikin mummunan yanayi na talauci, tsadar rayuwa da yunwa wanda hakan ya taimaka matuka wajen sabbaba ta’addanci, sace-sace da fashi da makami a yankin arewacin Najeriya, ba kuma komai ne ya haddasa hakan ba face tsare-tsaren mulkinsa wanda masana tattalin arziki suka jima suna gargadinsa cewa ba zai haifar da d’a mai ido ba.
  7. Bayan rashin tsaro, yunwa, talauci da tsadar rayuwa da wannan gwamnati ta haddasawa al’umma, gwamnatin ta samar da kabilanci na rashin adalci tsakanin bangaren Kudu da Arewa. Yadda gwamnatin ke fifita al’ummar kudanci tare da girmama su, amma Arewa kamar ba mutane ba, wannan kadai babban dalili ne da ya kamata a tsige shugaba Buhari domin mulkinsa yana kokarin rusa Najeriya.

Muna kiran ‘yan majalisarmu na Arewa da su had’a kansu wajen bijiro da wannan mataki don su ceci ‘yankinsu na Arewa, ko ba komai kun bar kyakkyawan tarihin da za a dinga yabon ku da shi ko bayan ranku, wannan mataki ko a wajen Allah Jihadi sunansa.

Indabawa Aliyu Imam

Exit mobile version