Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Buhari Ya Yi Rawar Gani Wajen Karya Boko Haram – Mohammed

Ministan yaɗa labarai da al’adu Lai Mohammed, ya ce Shugaban Ƙasa Buhari ya yi rawar gani sosai wajen shawo kan matsalar tsaro da karya laggon Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, al’ummar Arewa maso gabas sun daina biyan ‘yan Boko Haram haraji, suna rayuwa cikin walwala da kwanciyar hankali.

Lai Mohammed ya bayyana hakan ne a ganawarsa da kungiyar masu kamfanonin jarida a Najeria NPAN a Legas ranar Alhamis, akan matsalar tsaro a Najeriya musamman yankin Arewacin Najeriya.

Lai Mohammed yace kwace garuruwan da ‘yan Boko Haram ke yi ya zo karshe, babu wata karamar hukuma ko wani gari da ke a hannun Boko Haram a yanzu, saɓanin yadda abubuwa suke a baya lokacin PDP.

Sai dai ikirarin Ministan ya ci karo da rahotannin kwana-kwanan nan dake nuna mazauna yankin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma na biyan ‘yan bindiga haraji kafin su samu shiga gonakinsu su yi noma.

An ruwaito cewa manoman da aka kashe a Borno karshen makon da ya gabata sun ki biyan harajin ne, ya sanya har Ƙungiyar Boko Haram ta aikata musu abin da ta aikata.

Sai dai a bangaren MInista Lai Mohammed ya ce ‘yan bindigan sun daina haka saboda irin namijin kokarin da shugaba Muhammadu Buhari keyi, na ganin tsaro ya tabbata a ko ina a faɗin ƙasar nan.
“Kafin hawan shugaban kasa mulki, Boko Haram na iya shiga ko wani gari, musamman a Arewa, su kai hare-hare,” Yace “Birnin tarayya Abuja, Kano, Maiduguri, Jos, da Damaturu ne ake kai hari sosai.”
“Har tashohin mota, Coci-coci, Masallatai, da kasuwanni basu bari ba, amma a yau, abin ya zama tarihi.
“Amma yanzu ba haka bane. Abubuwa sun canza yau.” “A baya Boko Haram na kwace gari, tsige sarakunan gargajiya da kuma karban haraji, amma yanzu ba haka bane, wannan canjin ba wai kawai ya faru bane siddan, a’a nasarorin Sojoji ne karkashin jagorancin Shugaban Ƙasa Buhari.”

Exit mobile version