Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Hajjin Bana: Dubun Dubatar Maniyyata Ne Za Su Sauke Farali A Bana – Saudiyya

Rahotanni daga birnin Riyadh na kasar Saudiyya na bayyana cewar Hukumomi a ƙasar sun ce dubun dubatar masu ibada ne za su gudanar da aikin Hajji na bana, saɓanin adadi ƙalilan da suka yi aikin na 2020 da 2021.

Kafar yaɗa labarai ta Haramain Sharifain ta ambato mai magana da yawun ma’aikatar aikin Hajji yana cewa “Hajjin bana zai kasance na adadi mai yawa”.

Ci gaban na zuwa ne ‘yan kwanaki da Saudiyya ta cire dukkan dokokin kariya daga kamuwa da cutar korona, ciki har da ɗage wajabcin saka takunkumi a bainar jama’a.

Mutum 60,000 ne kacal suka gudanar da ibadar a shekarar 2021, yayin da ba su wuce 1,000 ba a 2020 sakamakon annobar korona da ta ɗaiɗaita harkoki a duniya.

Exit mobile version