Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Gwamnoni Sun Amince Da Zabin Shettima Mataimakin Tinubu

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun bayyana goyon bayansu ga Sanata Kashim Shettima a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar a zaɓen 2023.

Gwamnonin sun bayyana goyon bayansu ne bayan sun gana da Buhari a Daura.

A ranar Lahadi ne ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu ya sanar da tsohon gwamnan Borno Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai masa takarar mataimaki.

Shugaban gwamnonin na APC Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu da gwamnan Imo Hope Uzodimma waɗanda suka yi magana a madadin sauran gwamnonin sun ce da yawun bakinsu aka amince da Kashim a matsayin ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa.

Sun kuma yi alƙawalin yin aiki domin tabbatar da jam’iyyarsu ta APC ta yi nasara a zaɓen 2023.

Exit mobile version