Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

El Rufa’i Ya Fusata Da Zaben Shettima Da Tinubu Ya Yi

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Nasir El-Rufai bai ji dadin hukuncin da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yanke ba na zabar tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, a matsayin abokin takararsa.

Jaridar Daily Independent ta ruwaito daga wasu majiyoyi cewa shugabancin APC na kokarin ganin ta sasanta lamarin a cikin gida ta yadda ba zai fita waje kamar na jam’iyyar PDP da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ba.

Kamar yadda yake a yanzu, alaka ta yi tsami tsakanin Wike da dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar wanda ya sanar da Ifeanyi Okowa na jihar Delta a matsayin abokin takararsa.

Majiyoyin sun ce an takaita jerin sunayen abokan takarar Tinubu tsakanin El-Rufai daga arewa maso yamma da Shettima daga arewa maso gabas.

Yayin da mutane da dama suka fi raja’a kan cewa Tinubu zai zabi El-Rufai, kawai sai tsohon gwamnan na jihar Lagas ya sanar da Shettima a matsayin abokin takararsa.

Rahoton ya kuma kawo cewa an rubuta sunan Gwamna Simon Lalong na jihar Plateau cikin jerin sunayen koda Tinubu zai yanke shawarar yin tikitin Musulmi da Kirista. Amma da ya tabbatar lallai Musulmi dan uwansa yake son zaba a matsayin abokin takara sai aka gabatar da sunan El-Rufai da Shettima amma sai Tinubu ya zabi tsohon gwamnan na Borno wanda ya kasance daya daga cikin masu yi masa biyayya ba tare da tuntubar gwamnonin ba.

Duk da wannan ci gaban, gwamnonin sun kawar da fushinsu daga idon duniya sannan suka halarci gangamin kamfen din dan takarar gwamnan jam’iyyar a zaben Osun. Kuma sai PDP ta yi nasara a zaben.

Gwamna El-Rufai bai ji dadi ba game da hukuncin da Asiwaju Bola Tinubu ya dauka. An aika masa da jakadu amma ya kore su.” Duk da haka, ya halarci gangamin kamfen din gwamnan Osun a makon jiya saboda bai da matsala da takwaransa, Oyetola.

Majiyoyin sun kuma ce: “Amma ko shakka babu, ya yi fushi da Tinubu. Hakazalika wasu gwamnonin APC musamman na arewa sun tausayawa El-Rufai domin sun nanata cewa tunda sun mara ma Tinubu baya a zaben fidda gwani, toh lallai dole ya zabi daya daga cikinsu a matsayin abokin takara.

“Gwamnonin APC wadanda sune manyan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar na ganin Tinubu ya ci zarafinsu ta hanyar sanar da Shettima, tsohon gwamna a matsayin zabinsa ba tare da ya tuntube su ba.”

Exit mobile version