Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ba Na Goyon Bayan Tsige Buhari A Shugabanci – Sule Lamiɗo

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido, ya ce kiraye-kirayen da ake yi a kan tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari daga mulki bai dace ba kuma ba zai samu goyon bayansa ba ko kaɗan ba.

Lamido, wanda ya sanar da hakan ga manema labarai yayin taron rantsar da shugabannin kananan hukumomi 27 da aka zaba a jiharsa ta Jigawa.

Tsohon gwamnan wanda ya jaddada cewa bashi da wata matsala a tsakaninsa da shugaban kasa, ya kara da cewa yana kalubalantarsa ne saboda siyasa kuma iya fadin gaskiyarsa kenan.

Tsohon gwamnan, wanda ya yi magana a kan lamurran kasar nan daban-daban, ya tabbatar da cewa har yanzu lokacin cikar burinsa bai yi ba. Ya kara da cewa abinda jam’iyyar PDP take bukata a halin yanzu shine daidaituwa da kuma hadin kai baki daya.

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alkawarin kawo karshen matsalolin tsaron kasar nan, inda yace abubuwa ba za su cigaba da faruwa haka ba a 2021.

Shugaban kasa ya sanar da hakan ne yayin bayyana farin cikinsa a kan sakin daliban GSSS Kankara a jihar Katsina.

Shugaba Buhari ya tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa ba zai ci amanarsu ba. Ya ce hankalinsa yayi matukar tashi a kan matsalar rashin tsaron da wasu bangarorin kasarnan suke ciki.

Exit mobile version