Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

2023: Lamido Ya Fallasa Sunan Wanda Buhari Ke Son Zama Magajinshi

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP Alhaji Sule Lamido, ya ce yana hasashen samun wani juyi a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ta APC.

Lamido ya ce wannan juyi ne zai kai ga samar da tikitin shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Sule Lamiɗo ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya yarda cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne kadai dan takarar shugaban kasa na APC da zai iya ba jam’iyyarsa ta PDP ciwon kai.

Sai dai kuma, ya ce Tinubu ba zai taba zama dan takarar jam’iyyar mai mulki ba a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2023 saboda wasu dalilai masu karfi na siyasa da manufar APC.

“A yanzu haka, Tinubu na tsaka mai wuya daga ‘yan uwansa a kungiyar Afenifere wadanda suka fito karara suka nuna basa son shi da kuma gwamnonin APC da suka suna basa son shi saboda sun ce yana da izza da iko.

“Ku lura da maganganuna, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba. Na san tunanin mutumin. Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba. Na fada amma mutane basu yarda dani ba amma ku zuba ido ku gani”.

“Mu yi magana ta gaskiya, a yau Tinubu yana rawarsa ne shi kadai. Dubi abun da ya yi amma a yanzu suna ce masa a’a. “Idan kudu ta shirya lashe zabe, dan takara daya da zai iya fafatawa da PDP don kada su shine Tinubu. Yana da nufi mai kyau.

Exit mobile version