Majalisar dokokin jihar Kaduna ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Malam Nasir El-Rufai ya shigar gaban wata kotun tarayya inda yake kalubalantar rahoton Majalisar da ya zarge shi da almundahana da kuɗin gwamnati a lokacin mulkinsa.
Shi dai tsohon gwamnan na zargin Majalisar ne da take masa hakki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar.
Ita dai Majalisar dokokin jihar Kaduna a martanin da ta mayar, ta ce ta yi matukar mamaki ne yadda tsohon gwamnan ya ruga zuwa kotu, yana kalubalantar sakamakon binciken da kwamitinta ya gudanar, tana mai cewa yin hakan tamkar riga Malam Masallaci ne.
Mai magana da yawun Majalisar dokokin jihar Kaduna, Hon Henry Maraa, ya ce an mika rahoton ne domin a ci gaba da bincike kuma “za a kira shi”.
Game da zargin El Rufai na rashin ba shi dama domin kare kansa kuwa, Hon Maraa ya kara da cewa “za a bashi dama, za a kira shi, abin da muka lura da shi shi ne wadanda suka sa hannu da wadanda suka karbi kudi, da wadanda suka ba da kudi, idan an je gaba, idan an yi bincike idan an je kan shi, za a kira shi.”
Sai dai ya ce akwai abin mamaki a ce a yanzu tsohon gwamnan yana zuwa kotu “El Rufai da bai martaba kotu ba a wayi gari shi yake zuwa kotu.”
Ya dage cewa babu kuskure a binciken da suka yi sannan za su zauna da lauyoyinsu sannan kuma su mayar masa da martani.
A nasa bangaren, Mohammad Lawal, kakakin gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya ce takaddamar da ake ciki tsakanin El Rufai da sauran jami’an gwamnatinsa da kuma majalisar dokokin jihar Kaduna ta kunshi abubuwa da yawa – zargi da badakala.
“Ba za a yi saurin yanke hukunci ba, sai an zauna an bincika abin, sannan a gwamnatance ba wannan aikin kawai muka sa a gaba ba, ana samun wadanda suke cewa a bincika, ana samun wadanda suke cewa ba su yadda ba.” in ji shi.
Ya kara da cewa “ba za a hada baki da mu a cuci talakan jihar Kaduna ba.” kamar yadda kakakin ya bayyana.
Tun da farko dai daya daga cikin mukarraban tsohon gwamnan, ya ce bisa la’akari da suka yi cewa, Majalisar dokoki wuri ne da za a martaba doka, amma, a fahimtar su, sai ga mai dokar barci ya bige da gyangyadi, kamar yadda Malam Ja’afaru Sani tsohon kwamishina a gwamnatin El- Rufai ya shaida wa BBC.
A cewarsa, an kafa kwamitin bisa tsarin doka don haka ya ce bai kamata ace masu doka a gwamnatin dimokradiyya na take dokokin da suka ba da yancin fadin albarkacin baki ba.
“Abin da muke nema shi ne kotu ta yi watsi da wannan rahoto saboda ya take masa hakki.” in ji Malam Jafaru Sani.
Wannan al’amari na binciken tsohon gwamnan jihar Kadunan dai shi ne gaba-gaba cikin batutuwan da jama’a da dama a jihar ke tafka muhawara a kai, wani abu da wasu masana ke cewa manuniyace na irin wainar da za a toya a fagen siyasar jihar a zaben 2027.