Zunubi Ne Babba Tura Wa Rarara Kudin Waƙa – Limamin Haɗeja

Sheikh Yusuf Abdulrahman Ya’u, wanda shi ne babban limamin garin Hadejiya, jihar Jigawa, ya yi magana game da kudin da ake tarawa Dauda Kahutu Rarara, inda ya ce a halin da ake ciki, bai kamata a bijirowa talaka da maganar bada gudumuwa domin ayi wa shugaban kasa Buhari wata waka ba.

Shehin Malamin ya yi wannan bayani ne a wajen karatun littafin Adabul – Mufrad kamar yadda wani faifen bidiyo da ya shigo hannun mu ya bayyana.

Limamin ya ke tsokaci ya na cewa: “Kuma ana wannan yanayin wani ya zo ya na cewa a ba shi N1, 000 zai fitar da wani abu.”
“Kai ka ji wani rashin hankali, mu na cikin damuwa da bakin ciki, ace za a fitar da wata waka. Ka ji wata masifa fa.” Inji Sheikh Yusuf Abdulrahman.

“Ba a bar ka da radadi ba, shi kuma wani Naira dubu-dubu ya ke nema domin ya fitar da wata muhimmiyar waka wanda talakawa za su yi dariya.”

Ganin irin halin da ake ciki na tsadar rayuwa da kudin kayan abinci, malamin ya ce, “Yanzu talaka ya daina dariya, idan ka gan shi yanzu sai hawaye ya ke yi.” Malamin ya ce rashin sanin abin da ya kamata ne a aikawa Mawakin kudin rera waka.

“Da wannan N1000, da masallain unguwarku, ka saye kwan lantarki da ya fi alheri.”

A sa kan fanfo ko fanka a masallaci ya fi alheri a kan a ba Rarara kudin waka. A karshe Shehin Malamin ya ce wakar da za a rangada ba za ta yi wani dadin a zo a gani ba, saboda halin ƙuncin da ake ciki.

Labarai Makamanta