Zulum Ya Fi Ni Zama Alheri A Jihar Borno – Shettima

Tsohon Gwamnan Jihar Borno Sanata Kashim Shettima mai wakiltar Borno ta Tsakiya a Majalisar Dokoki ta kasa ya tabbatar da cewa zabar Gwamna Babagana Zulum a matsayin wanda zai gaje shi ba don wasu dalilai na kashin kansa ba amma don maslahar jihar ta Borno ne.

Ya yi nuni da cewa Farfesa Zulum ‘ya fi shi a duk wasu bangarori.

Shettima ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wata makala a wajen taron laccar Jama’a da Hadin gwiwar Kungiyoyin Matasa suka shirya a Birnin Kebbi tare da taken: “Cigaban Matasa da Jagoranci.”

Ya bayyana cewa ya tsallake matsaloli da yawa har ya kai ga ya zabi wanda zai gaje shi, Farfesa Babagana Umara Zulum, wanda kuma ya bayyana a matsayin amintaccen dan siyasa.

Tsohon Gwamnan ya shawarci shuwagabanni da su fahimci cewa shugabanci ya kasance amana daga Allah Madaukakin Sarki, ya kara da cewa, ya kamata a kalle shi a zama na wani lokaci wanda dole ne mutum yayi bayani a lahira.

“A matsayinmu na shugabanni, dole ne mu sanya tunanin jagoranci, horar da matasa iyar gwargwadon ikonmu, la’akari da cewa ba za mu iya rayuwa har abada ba,” ya ba da shawara.

Musamman, kan nasiha, Shettima ya lura cewa babu abin da ya fi hatsari fiye da damka ragamar mulki ga mutanen da ba su da ilimi.

Ya kuma yi korafin cewa yawancin Matasa ba su da ilimi ko dabarun kasuwanci.

Ya jaddada bukatar matasa su jajirce wajen neman ilimi, don walwala da fitar da kasar zuwa inda ake bukata.

Shettima ya yi kira da a tallafawa talakawa da tattalin arziki don bunkasa ci gaban kasar baki daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply