Zazzau: Mutane Biyar Da Guda Zai Zama Sarki

Hankalin ?an Najeriya musamman arewacin ?asar na dakon sanarwar sabon sarkin Zazzau da zai gaji Sarkin Zazzau marigayi Alhaji Shehu Idris.

A ranar Lahadi ne Allah Ya yi wa mai Martaba Sarkin Zazzau Dokta Shehu Idris rasuwa bayan shafe shekaru 45 kan gadon sarautar Zazzau.

Marigayin wanda shi ne sarkin Zazzau na 18 a daular Fulani, ya rasu ne yana da shekara 85 a duniya.

Bisa tsarin sarautar Zazzau ana za?en sabon sarki ne daga gidajen masarautar guda hu?u – wato daga Gidan Mallawa da Gidan Barebari da Gidan Katsinawa da kuma Gidan Sullu?awa.

Masanin tarihin masarautar Zazzau kuma daraktan gidan Tarihi na Arewa da ke ?ar?ashin Jami’ar Ahmadu Bello, Shu’aibu Shehu Aliyu ya shaida wa BBC cewa wa?annan gidajen ne ke turo ?an takara ?aya da zai nemi sarautar Zazzau ga masu za?en sabon sarki.

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ne zai za?i sabon Sarkin Zazzau, cikin mutum uku daga cikin ?a?an gidan masarautar Zazzau da masu na?in sabon sarki suka tura masa.

Mutum biyar daga cikin wa?annan gidajen da ake ganin cikinsu za a za?i sabon sarkin Zazzau na 19, sun ha?a da:

Turakin Zazzau – Aminu Shehu Idris

Aminu Shehu Idris ya fito ne daga gidan Katsinawa, Gidan Malam Idris Auta. Shi ne babban ?an margayi Alhaji Shehu Idris.

Shi yake ri?e da sarautar Turakin Zazzau a yanzu.

Turakin Zazzau wanda ma’aikaci ne a kamfanin mai na NNPC, ?wararre ne a harkar kasuwar fetur da gas a Najeriya.

Kasancewarsa babban ?an marigayi Alhaji Shehu Idris, ana ganin yana iya zama sabon sarkin Zazzau.

Yariman Zazzau – Mannir Jafaru

Yana iya zama sabon sarkin Zazzau saboda girmama shi da ake da kuma sanayyar da yake da ita ko ba don ma sarautarsa ta Yariman Zazzau ba.

Yariman Zazzau Mannir Jafaru tsohon shugaban hukumar NIMASA ne kuma tsohon kwamishina ne a jihar Kaduna.

Mannir Jafaru, ya fito ne daga gidan Barebari, kuma ?an tsohon sarkin Zazzau ne Malam Jafaru ?an Isiyaku wanda ya yi sarki daga 1937 zuwa 1959.

Wasu na ganin wannan wata dama ce ga Yariman ya gaji mahaifinsa.

Magajin Garin Zazzau – Ahmad Nuhu Bamalli
Ahmed Nuhu Bamalli jakadan Najeriya a Thailand

Ahmad Nuhu Bamalli ya fito ne daga gidan Mallawa, kuma shi ne yanzu Magajin Garin Zazzau, babbar sarauta a Masarautar Zazzau.

Ambasada Ahmad jika ne ga Nuhu Bamalli tsohon Magajin Garin Zazzau kuma tsohon minista a Najeriya.

Magajin garin Zazzau wanda masanni shari’a ne da diflomasiyya shi ne jakadan Najeriya a Thailand a yanzu.

Saboda girman sarautarsa ta Magajin Garin Zazzau da kuma kusancinsa da gwamnati ana ganin zai iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.

Iyan Zazzau – Bashir Aminu

Iyan Zazzau Bashir Aminu ya fito ne daga gidan Katsinawa ?an tsohon Sarkin Zazzau na 17 Malam Muhammadu Aminu.

Iyan Zazzau ya ta?a rike sarautar Dan Madamin Zazzau kafin ya zama Hakimin Sabon Gari.

Bashir Aminu ana ganin yana iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.

Shitu Ibrahim Dikko – Dangaladiman Wazirin Zazzau

Dangaladiman Wazirin Zazzau Hakimin Gundumar Gabasawa Alhaji Shitu Ibrahim Dikko ya fito ne daga gidan Sullu?awa ?aya daga cikin gidajen da ke da gadon sarautar Zazzau.

Dangaladiman Wazirin Zazzau ?aya daga cikin jikokin Sarkin Zazzau ne marigayi Malam Abdussalam daga gidan Sullu?awa wanda ya yi mulki tsawon shekara hu?u tsakanin 1853 zuwa 1857.

A 2008 marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris ya ba shi sarautar Dangaladiman Wazirin Zazzau kuma gwamnan Kaduna Malam Nasir El- Rufa’i ya na?a shi Hakimin Gabasawa a yankin Kaduna ta Arewa a 2018.

Kasancewarsa daga gidan Sullu?awa ana ganin yana iya zama sabon Sarkin Zazzau na 19.

Masu za?en sabon Sarkin Zazzau

Masanin tarihin masarautar Zazzau kuma daraktan gidan Tarihi na Arewa da ke ?ar?ashin Jami’ar Ahmadu Bello, Shu’aibu Shehu Aliyu ya ce majalisar masu za?en sarkin Zazzau ta ?unshi mutum biyar.

Su za su zauna su tantance wa?anda suka cancanta daga nan su tura wa gwamnan jihar Kaduna sunayen mutum uku domin ya za?i ?aya a matsayin sabon sarki. Don haka sai abin da gwamna ya yanke.

Masanin ya ce masu za?en sabon sarkin sun ha?a da Makaman Zazzau, Alhaji Muhammad Abbas da Fagacin Zazzau, Alhaji Umar Muhammad da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu da Limamin Kona Sheikh Muhammad Sani Aliyu da kuma Limamin Gari, Sheikh Dalhatu ?asim.

Related posts

Leave a Comment