Zazzau: Masu Zaɓen Sarki Sun Yi Mubaya’a Ga Bamalli

‘Yan majalisar nadin sarakunan Zazzau sun amince da zabar Ahmed Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau, jim kaɗan bayan sanar da naɗin nashi.

An nada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sarkin Zazzau a ranar Laraba, 7 ga watan Oktoban 2020. Bayan rasuwar Sarki Shehu Idris da yayi shekaru 45 a karagar mulki (1975-2020).

Jim kadan bayan Sakataran Gwamnatin jihar Kaduna ya isa fadar sarkin Zazzau da sanarwar nadin sabon sarkin, ‘yan uwa da abokan arziki da al’ummar Zazzau suka yi ta tururuwar zuwa fada cike da farin ciki.

Alhaji Munir Ja’afaru, Yeriman Zazzau kuma daya daga cikin manema kujerar ya isar da sokon taya murnarsa da kuma amincewarsa dari-bisa-dari da nadin, har yana cewa Allah ne ke bayar da mulki ga wanda yaso.

‘Yan majalisar zaben sarkin sun hada da Limamin Kona; Sani Aliyu, Limamin Juma’a; Dalhat Kasim, Makama Karami; Mahmood Abbas, Fagacin Zazzau; Umar Mohammed da Wazirin Zazzau; Ibrahim Aminu.

Kamar yadda aka sani, masarautar Zazzau nada gidajen sarauta 4, sune Gidan Katsinawa, Barebari, Mallawa da kuma Sullubawa.

Sabon Sarki Ahmed Bamalli dan asalin gidan Mallawa ne, wanda a tarihi, shekaru 100 kenan rabon da sarauta ta koma gidan, tun bayan mutuwar kakansa, Alu Dan Sidi, sarki na 13 a shekarar 1920.

Bayan bada sanarwar, garin ya dinke da farin ciki da murna tare da kabbarori. Jama’a da dama sun dinga fatan alkhairi tare da taya sabon Sarkin Murna wannan karagar mai dumbin tarihi da ya haye.

Labarai Makamanta

Leave a Reply