Zargin Ta’addanci: PDP Ta Bukaci A Kori Pantami

Babbar jam’iyyar hamayya ta PDP, ta ro?i hukumar tsaro ta farin kaya DSS, da su gaggauta gayyatar ministan sadarwa, sheikh Isa Pantami, domin ya amsa tambayoyi kan zargin da ake masa na goyon bayan ?ungiyoyin ta’addanci, sannan da ?aukar matakan da suka dace a kanshi.

Hakanan kuma jam’iyyar ta ba shugaba Muhammadu Buhari shawara a kan ministan, tace yakamata ya kula sosai da wannan lamarin, ba abin wasa bane matu?ar zargin ya tabbata to a gaggauta ?aukar matakin da ya dace.

Jam’iyyar ta PDP ta bayyana matsayarta ne a wani jawabi data fitar ?auke da sa hannun kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan , ranar Lahadi kuma aka rarraba ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Kola Ologbondiyan yace: “Jam’iyyar mu ta damu matu?a da lokacin da ake ?auka kan wannan lamarin da kuma jayayya da ministan sadarwa, wanda keda ajiyayyun bayanan gwamnati, da bayanan wasu ?ai?aikun mutane masu ?ima.”

“PDP ta damu matu?a da zargin da mutane ke masa, kuma muna gudun kada ministan ya yi abinda bai dace ba wajen ba wasu daba ‘yan ?asa ba dama suzo su mamaye rijistar NIN ?in da ake yi yanzun, su zama yan ?asa.”

Jami’iyyar ta PDP na kira ga DSS su gudanar da bincike kan zarge-zargen, wanda ya jawo cece-kuce da tsoro sosai musamman ma saboda ?aruwar hare-haren yan bindiga da sauran ayyukan ta’addanci a?asar nan.”

Sai dai a ?arshen makonnan minista Pantami yace bai ta? zama mai tsattsauran ra’ayi ba kuma shi baya kan wasu maganganu da yayi a baya. Ya kuma ce babu wani malamin addinin musulunci a baya ko a yanzun da ya ?alubalanci ayyukan Boko Haram kamar shi.

Pantami ya fa?i haka ne a lokacin gudanar da tasirin watan Ramadana da yake gudana a masallacin An-Noor, Abuja.

Related posts

Leave a Comment