Zargin Sojoji Kiristoci: Rundunar Soji Ta Gargadi Gumi

Rundunar Sojin Najeriya cikin fushi ta ja kunnen fiaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi, da ya guje zubdawa rundunar mutunci ta hanyar yin maganganu barkatai ba tare da taunawa ba.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya janar Mohammed Yerima ya sanar da hakan a wata takarda da rundunar ta fitar kuma aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja, inda aka ja kunnen malamin da ya kiyaye yadda zai dinga kwatanta rundunar sojin.

“Hankalin rundunar sojin Najeriya ta kai kan wani bidiyo da ke nuna fitaccen malami Sheikh Ahmed Gumi yana zargin sojojin da ba musulmi ba da harar ko kuma kisan Fulani ‘yan bindiga.”

“A wannan bidiyon, an ga malamin yana sanar da ‘yan bindiga cewa sojojin da ke kai musu hari yawanci ba musulmi bane. Ya kara da bayyana cewa su sani, sojoji sun rabu, musulmi da wadanda ba musulmi ba.

“Yayin da rundunar bata son hada zantuka da Shehin malamin, akwai matukar amfani a san cewa rundunar bata tura dakarunta aikin kabilanci ko addini.

“A don haka take kira ga Sheikh Gumi da sauran masu fadin ra’ayoyinsu da su gujewa saka rundunar cikin irin wadannan lamurran domin gujewar zubewar mutuncin daya daga cikin mafi nagartar ma’aikatu a kasar nan.”

Related posts

Leave a Comment