Zargin Sojoji: Dattawan Arewa Sun Nesanta Kansu Da Kalaman Gumi

Wata Kungiyar dattawan Arewa a ranar Laraba sun nesanta kansu daga maganganun kwanan nan da aka alakanta da malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi, wanda ya zama jakadan sulhu da ’yan fashi a dazuzzukan da ke fadin jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, da Neja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa a yayin daya daga cikin irin wadannan tarurrukan, ya yi zargin cewa sojoji wadanda ba Musulmi ba sun aiwatar da kisan gilla a wasu garuruwa, lamarin da ya fusata su.

“Abin da nake so ku fahimta shi ne, sojojin da ke da hannu a cikin yawancin laifukan ba Musulmi ba ne. Ku sani, sojoji suna da musulmai kuma suna da wadanda ba musulmai ba.

Wadanda ba Musulmai ba ne ke haifar da rudani don kawai a haddasa rikici,” in ji Gumi. Ya fadi hakan ne ga wata tawaga karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Neja a kan aikin sulhu don sakin daliban Kagara da aka sace. Amma dattawan da ke karkashin kungiyar Dattawan Arewa maso Gabas kan ci gaban Zaman Lafiya (NEEPD) sun ce zargin na Gumi bai wakilci matsayin yankin ba , suna masu cewa dole ne jama’a su yi wa abun kallo a matsayin “ra’ayin kansa”.

Yayin da take kira ga jama’a da suyi watsi da wannan zargi, kungiyar ta NEEPD a cikin wata sanarwa daga jagoranta, Zana Goni, ta sha alwashin yin watsi da duk wani yunkuri na mutum ko wata kungiya kan sojin. A cewarsu, ya zama dole manyan kungiyoyin Arewa su yi Allah wadai da ikirarin Gumi mai hadari, don kada mutane suyi tunanin cewa yana magana ne da yawun yankin.

Duba ga kalaman nasa, ta iya yiwuwa Gumi na kare fashi da makami ne da duk abin da ke da nasaba da laifin. A gefe guda, babban shehin malamin nan Ahmad Gumi ya bayyana cewa ?an bindiga ba ?an ta’adda ba ne domin fa?ansu; “fa?an cikin gida”. Ya dai yi wannan lafazi ne a wata hira da yayi da gidan wani talabijin a ranar Litinin inda ya tabbatar da cewa ?an bindigar ba sa sha’awar kisan mutane, kuma ko da ?an ka?an ?in da suka kashe, sun yi ne ba a bisa son ransu ba.

A wasu jihohi dai na Arewa maso yamma da kuma Arewa maso tsakiyar ?asar nan, ana ta fama da cigaba da samun hare-hare na ?an bindiga wa?anda ke zagayawa ?auyuka suna kai farmaki a yayin da ba sa kan hanyoyi kamar yadda suka saba domin sace matafiya.

Related posts

Leave a Comment