Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa bayan da Honorabul Aliyu Sani Madaki ya kai kudurin gaban majalisar wakilai ta nemi a dakatar da Yarjejeniyar Samoa da ake zargi da Auren Ji’nsi.
Rahotanni sun bayyana Majalisar Wakilai ta nemi Gwamnatin tarayya da ta dakatar da aiwatar da yarjejeniyar Samoa bisa zargin Maganar “LGBTQ
Majalisar ta umarci kwamitinta mai kula da tsare-tsare na kasa da ya binciki yarjejeniyar cikin makonni hudu.
Kudurin Majalisar ya biyo bayan kudirin da shugaban marasa rinjaye, Aliyu Madaki, da wasu mutane 87 suka Gabatar a zauren majalisar a Yau Talata.