Wata kungiya mai rajin kare mutuncin Najeriya (Concerned Nigerians) ta yi Allah wadai da yunkurin shugaba Buhari na son nada Lauretta Onochie a matsayin kwamishiniya a hukumar zabe ta kasa (INEC), inda Ƙungiyar ta ɗauki matakin kai ƙarar Buhari ƙasar Amurka.
Kungiyar ta roki Amurka, Ingila, da sauran ma su fada a ji a duniya a kan su kawowa Najeriya agaji saboda Buhari ya na shirin lalata siyasar kasa da kassara hukumar zabe mai zaman kanta INEC.
A takardar da kungiyar ta rubuta ranar Alhamis, 14 ga watan Oktoba, ta sanar da Amurka da ƙawayenta cewa nadin Lauretta ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Kowa ya san ‘yar siyasa ce da ke dauke da katin shaidar zama mamba a jam’iyyar APC mai mulki. “Ba iya wannan ne kadai matsalar ba, ta yi kaurin suna wajen ragargaza da cin mutuncin duk wanda ya soki jam’iyyar APC”.
“Nada Lauretta, hadimar shugaban kasa, a matsayin kwamishiniya a INEC mai wakiltar jihar Delta ya sabawa kundin tsarin mulki kuma yunkuri ne na lalata kima da martabar hukumar zabe,” a cewar takardar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Deji Adeyanju.
Har yanzu yunkurin shugaba Buhari na son nada Lauretta na cigaba da haifar da cece-kucea cikin kasar.
Babbar jam’iyyar adawa, PDP, da sauran dumbin ‘yan Najeriya sun nuna rashin amincewa da niyyar shugaba Buhari ta nada Lauretta a mukami mai muhimmanci kamar kwamishiniya a hukumar INEC.