Babbar Kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta ba Sanata Ali Ndume kwanaki 21 don ya gabatar da tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrasheed Maina, wanda kusan karo na 10 kenan bai je shari’a kotun ba tun watan Satumba 2020.
Babban mai shari’a Okon Abang, ya bada wannan umurnin ga Sanata Ali Ndume a zaman kotun na yau wanda daman sanatan shine tsayayyen da Maina ya gabatar wa kotun, don matsawar bai gabatar da wanda yake karewa ba a kotu ranar 18 ga watan Nuwamba, kotu za ta damke shi.
Hukumar EFCC da sanata Ndume sun roki kotu da ta bada damar damko Maina a ranar Litinin, Amma Alkalin kotun yace ba zai sa a damko Maina ba, ba tare da rike tsayayyensa ba a hannu. Yace zai bai wa Sanata damar wasu satittuka don nemo wanda yake karewa ya kuma gabatar da shi a kotu.
Duk da Maina bai gabata a kotu ba, masu mara masa baya sun ce Alkalin na kokarin shafa masa bakin fenti tare da nuna son kai a kotun. Duk da wani bidiyon Maina yayi ta yawo a yanar gizo, inda Maina ke sanar da jinyar da yake yi ta kafarsa, kuma yace ba zai bayyana gaban kotu ba har sai likitoci sun tabbatar da lafiyarsa.