Zargin Cin Hanci: Za A Cigaba Da Shari’ar Ganduje Da Matarsa Ko Basu Halarci Kotu Ba – Babbar Kotun Kano

images 2024 03 06T195109.222

Babbar Kotun Jihar Kano ta ce za a ci gaba da shari’ar Shugaban Jam’iyyar APC Abdullahi Ganduje da wasu da ake zargi da cin hanci da rashawa ko da basu Halarci Zaman Kotu ba.

Gwamnatin jihar ta shigar da karar Ganduje da matarsa ??Hafsat Umar dangane da tuhume-tuhume guda takwas; Abubakar Bawuro; Umar Abdullahi Umar; Jibrilla Muhammad, Lamash Properties Limited, Safari Textiles Limited, da Lasage General Enterprises Limited. Laifukan sun hada da zargin karbar rashawa, almubazzaranci, da karkatar da ku?a?en jama’a da suka kai biliyoyin naira.

Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu ta yi watsi da bukatar gwamnatin jihar na neman A tilasta wa wa?anda ake ?ara Zuwa zaman kotu ta bayyana cewa “za’a cigaba da shari’ar wa?anda ake tuhumar ko da ba su nan,” in ji ta.

Mai shari’a Amina Adamu-Aliyu Ta dage cigaba da sauraron karar har zuwa ranar 23 da 24 ga watan Oktoba domin sauraren karar farko da kuma babban tuhume-tuhumen da aka shigar Dangane da Ganduje da sauran mutanen.

Related posts

Leave a Comment