Zanga-zangar SARS Shirine Na Kifar Da Gwamnatin Buhari – Sheikh Jingir

Babban Malamin Addinin Musulunci kuma jigo a ?ungiyar Izala (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya yi i?irarin cewa zanga-zangar kawo ?arshen sashe na musamman mai ya?i da fashi da makami (SARS) da ke gudana a halin yanzu ?ullallen shiri ne don ruguza mulkin shugaban ?asa Muhammadu Buhari da arewacin ?asar nan.

“Abune a bu?e, wannan zanga-zangar shirin wargaza gwamnatin Buhari da kuma rushe ?aukacin arewacin ?asar nan.
”Na fa?i haka saboda masu zanga_zangar sun bu?aci a rushe sashe na musamman ya?i da fashi da makami(SARS) kuma an biya musu bu?atarsu amma har yanzu sun cigaba da zanga-zangar har wasu na kiran shugaban ?asa da yayi murabus.

”Wannan na nuni da cewa akwai wani mummunan abu a ?oye a cikin tafiyar,” Malamin yayi wannan i?irari lokacin da ya ke gabatar da hu?ubar Sallar Juma’a a Masallacin ?antaya da ke Jos; babban birnin jihar Plateau.

Sannan ya cigaba da cewa; “ba ma goyon bayan wannan tafiya ta zanga-zangar kawo ?arshen sashe na musamman mai ya?i da fashi da makami saboda babu gaskiya acikinta. An saka siyasa a ciki.

”Muna kira ga mutane da su ?auracewa wannan tafiyar. ”Abin da muke bu?ata shine addu’a don cigaban ?asar mu da kuma ganin ?arshen rashin tsaro da ya addabi al-ummomi da dama.”

Sheikh Jingir ya ce tafiyar zata kawo koma baya ga ?asa a halin da ake ciki na fama da matsalar tsaro a sassan ?asar nan, musamman a arewa. A karshe, ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya gaggauta ?aukar mataki tun kafin abu ya zo ya gagara.

Related posts

Leave a Comment