Babban Malamin Addinin Musulunci kuma Shugaban Majalisar Malamai na ƙungiyar Izala (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya yi iƙirarin cewa zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami (SARS) da ke gudana a halin yanzu ƙullallen shiri ne don ruguza mulkin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da arewacin ƙasar nan.
“Abune a buɗe, wannan zanga-zangar shirin wargaza gwamnatin Buhari da kuma rushe ɗaukacin arewacin ƙasar nan.
”Na faɗi haka saboda masu zanga_zangar sun buƙaci a rushe sashe na musamman yaƙi da fashi da makami(SARS) kuma an biya musu buƙatarsu amma har yanzu sun cigaba da zanga-zangar har wasu na kiran shugaban ƙasa da yayi murabus.
”Wannan na nuni da cewa akwai wani mummunan abu a ɓoye a cikin tafiyar,” Malamin yayi wannan iƙirari lokacin da ya ke gabatar da huɗubar Sallar Juma’a a Masallacin Ƴantaya da ke Jos; babban birnin jihar Plateau.
Sannan ya cigaba da cewa; “ba ma goyon bayan wannan tafiya ta zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami saboda babu gaskiya acikinta. An saka siyasa a ciki.
”Muna kira ga mutane da su ƙauracewa wannan tafiyar. ”Abin da muke buƙata shine addu’a don cigaban ƙasar mu da kuma ganin ƙarshen rashin tsaro da ya addabi al-ummomi da dama.”
Sheikh Jingir ya ce tafiyar zata kawo koma baya ga ƙasa a halin da ake ciki na fama da matsalar tsaro a sassan ƙasar nan, musamman a arewa. A karshe, ya yi kira ga Shugaba Buhari da ya gaggauta ɗaukar mataki tun kafin abu ya zo ya gagara.