Zanga-Zangar SARS: Fatima Ganduje Ta Shawarci Masu Zanga-Zanga

Fatima Ganduje Ajimobi ɗiyar Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, kuma Surukar tsohon Gwamnan Jihar Oyo Sanata Ajimobi, ta sharwaci Matasa da ke cigaba da kara-kaina a Zanga-zangar kawo karshen SARS, da cewar akwai hanya mafi sauki da za su bi wajen samar da sauyi ba tare da yin Zanga-zanga ba.

A wani rubutu data wallafa a shafinta na Instagram ranar Asabar, 17 ga Oktoba, tayi kira ga matasan su mallaki katin zaben su sannan kuma bayan sun kaɗa kuri’arsu su tabbatar an kirga kuri’ar tasu.

“Kuyi zabe kuma kada ku bar mazabar har sai an ƙirga kuri’arku. Kuyi gangami ku raka kuri’unku,” Fatima ta rubuta.
“Ku tsaya kai da fata a wajen tattara sakamako sannan ku tabbatar an ƙirga kuri’arku. Matasa sune mafiya rinjaye kuma su za su ceto kasar mu Najeriya. (#ENDSARS #ENDOPRESSION #FGA),” ta sake rubutawa.

Anasa bangaren, mijinta Idris Ajimobi ya yi kira ga matasa da su tabbatar sun tanadi katin zabensu don tunkarar babban zaben 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply