Zanga-Zangar SARS: Babu Inda Na Yi Kiran Kaddamar Da Yaki – Yerima

Jagoran Kungiyar Matasan Arewa Alhaji Yerima Shettima ya nesanta kanshi da wani labarin ƙanzon kurege da wasu Jaridun kudancin Najeriya suke yaɗawa na cewar wai ya yi kiran ƙaddamar da yaƙi ga jama’ar Kudu, muddin Zanga-zangar SARS ta yi nasarar kifar da Gwamnatin Shugaban ƙasa Buhari.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da Kungiyar cigaban Matasan Arewan ta fitar ta hannun Babban Lauyan Ƙungiyar Barista Abubakar Liman kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

Sanarwar ta kara da cewar wancan bayani da Jaridun suka ɗauka, wani shiri ne na cin zarafi da ƙoƙarin shafa baƙin fenti ga Jagoran Matasan Arewa Yerima Shettima.

Ga duk wanda ya san Alhaji Yerima Shettima ya san shi a matsayin ɗan kasa nagari mai tattalin ganin zaman lafiya a tsakanin jama’ar Najeriya, saboda haka wancan labari karya ce muraran aka shirya domin ɓata sunan shi.

Shugaban Matasan na Arewa bai taɓa shiryawa ko ɗaukar nauyin yin wata zanga-zanga ba, shi ɗan ƙasa nagari ne wanda ya ke bi tsari da dokokin ƙasa sau da ƙafa.

Muna a matsayin ‘yan Arewa masu kishin Arewa, waɗanda ba za su lamunci dukkanin wani yunkuri na wulakanta yankin ba, amma a bisa ga tsari da doka ba hanyar tashin hankali ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply