Zanga-zangar SARS: An Hallaka Direban Minista

An kashe direban ministan ƙwadagon Najeriya, Fetus Keyamo a zanga-zangar EndSars a ranar Laraba a Abuja.

A wani sakon Twitter da ya wallafa ministan ya ce, an kashe direbarsa Mr. Yohanna Shankuk, bayan ya ajiye mota sakamakon datse titi da masu zanga-zanga suka yi, sai ya yi kokarin takawa da ƙafa zuwa ofishinsa.

Mutane da dama ne suka jikkata a zanga-zangar ta EndSars bayan wasu matasa dauke da makamai sun afkawa gungun mutanen da ke gangami akan titi.

Hotuna da bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta sun nuna yadda matasan suka ɓullo daga wani wuri daban ɗauke da sanduna suna kai wa masu zanga-zangar hari.

Ƙungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta yi zargin cewa wasu ne suka ɗauki nauyin matasan domin tarwatsa zanga-zangar.

Kazalika, sun farfasa gilasan motoci kuma an ji wa wasu mummunan rauni.

Kusan mako guda kenan ana yin zanga-zanga a wasu jihohin Najeriya domin neman yin gyara ga ayyukan ƴan sanda a ƙasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply