Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu yace bai dace ƙungiyar ƙwadago ta kira yajin aiki a watanni tara na farkon mulkinsa ba.
Yayin da yake jawabi a birnin Legas ranar Alhamis lokacin ƙaddamar da layin dogo na Red line, shugaba Tinubu ya yi kira ga ƙungiyar ƙwadagon ƙasar ta tabbatar da zaman lafiya, yana mai cewa ba ita ce kaɗai muryar ‘yan NAjeriya ba.
Ƙungiyar NLC da ta kira ga mambobinta su gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar a ranakun 27 da 28 ga watan Fabrairu, don nuna adawa da tsadar rayuwa da matsain tattalin arziki da ake fuskanta a ƙasar.
To sai dai bayan zanga-zanga a rana ta farko, ƙungiyar ta janye zanga-zanagr da ta shiya yi a rana ta biyu, tare da bai wa gwamnati wa’adin mako biyu, ta ɓullo da matakan rage tsadar rayuwa a ƙasar.
To sai dai shugaba Tinubu ya ce bai kamata ƙungiyar ta shirya yajin aiki a watanni tara na mulkinsa ba.
“Ya kamata NLC ta fahimci cewa komai muka san ‘yanci da haƙƙinmu, bai kamata ta kira yajin aiki a watanni taran farkon mulkina ba”, in ji Tinubu.
“Idan kuna son shiga zaɓe, ku jira 2027. in ba haka ba kuwa, a ɗore da zaman lafiya, saboda ba ku kuɗai ba ne muryar ‘yan Najeriya.”