Zanga-zangar Kawo Ƙarshen SARS: Iyalan Buhari Dana Osibanjo Sun Goyi Baya

Iyalan Shugaba Buhari da na mataimakinsa Osinbajo sunbi sahun masu zanga-zanga
Zahra Buhari da Kiki Osinbajo sunbi sahun masu zanga-zanga kawo karshen zaluncin jami’an SARS.

Iyalan Shugaban Najeriya da na mataimakinsa wato Zahra Buhari da Kiki Osinbajo, sun shiga zanga-zangar kawo ƙarshen azabtarwar da ake zargin ‘yan sandan SARS ke yi a Najeriya.

‘Yar gidan Shugaba Buhari, wato Zahra, ta wallafa wani hoto a shafinta na Instagram, wanda masu gudanar da irin wannan zanga-zanga musamman a shafukan sada zumunta suke wallafawa na kawo ƙarshen ‘azabtarwar’.

Ita kuwa ‘yar gidan Osinbajo, ta yi amfani da duka mau’du’an guda biyu, wato na #endpolicebrutality da kuma na #endsars, ma’ana tana goyon bayan kawo ƙarshen ‘azabtarwar’ da ‘yan sanda ke yi da kuma soke rundunar SARS.

Labarai Makamanta

Leave a Reply