Zanga-Zangar Endsars: Buhari Ya Girbi Abin Da Ya Shuka Ne – Shugaban Talakawa

An bayyana cewar ?azamar Zanga-Zangar Endsars da ke cigaba da gudana a wasu sassa na Najeriya, girbi ne na shukar da Buhari ya yi a baya.

Shugaban Talakawan Najeriya Alhaji Imrana Nas ne ya bayyana hakan, a yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Kaduna dangane da Zanga-Zangar Endsars.

Imrana Nas ya cigaba da cewar kowa ya san irin matsayin da Buhari ya ?auka a baya na jagorantar Zanga-Zanga a duk lokacin da wani ?an abu ?alilan ya faru lokacin mulkin PDP a baya.

“Tarihi ba zai manta lokacin da Buhari ya jagoranci Zanga-Zanga zamanin mulkin Shugaba Jonathan saboda ?arin Farashin Mai da aka yi a wancan lokaci.
“Wa?annan Matasa da su aka yi amfani wurin cin mutunci da zarafin jama’a a wancan lokacin, kuma a yanzu sune suka dawo suna rama wa kura aniyarta.

Sai dai kuma Shugaban Talakawan ya bukaci masu Zanga-Zangar da su ajiye makamansu tun da gwamnati ta saurari koken na su har ta amince da rusa SARS, sai dai idan dama da akwai wata ?oyayyiyar manufa a ?asa ne.

Imrana Nas ya kuma yi kira ga dukkanin jama’ar Najeriya da su dage wajen addu’o’i na Allah ya kawo sauki dangane da halin da ?asa ta shiga na ta?ar?arewar tsaro da annobar talauci.

Related posts

Leave a Comment