Bayan lashe kwanaki da wasu ‘yan Najeriya suka yi suna gudanar da Zanga-zangar neman a soke rundunar SARS mai yaƙi da manyan laifuka, daga bisani haƙarsu ta cimma ruwa inda Gwamnatin tarayya ta amince da soke rundunar.
Babban Shugaban ‘yan sandan Najeriya Mohammed Adamu, ya soke rundunar da ke yaƙi da fashi da makami a Najeriya wato SARS.
Ya bayyana hakan ne a wani jawabin kai tsaye ga manema labarai a ranar Lahadi.
Soke rundunar ya biyo bayan jerin zanga-zangar da aka ɗauki kwanaki ana yi a wasu jihohin ƙasar, inda ko a yau ma sai da aka yi irin wannan zanga-zangar a Ingila.
‘Yan ƙasar dai suna zargin rundunar ta SARS da azabtarwa da kisa ba bisa ƙa’ida ba da saɓa dokokin aiki.
A baya dai gwamnatin ƙasar ta ce ba za ta soke rundunar ba, sai dai ta yi mata sauyi ko kuma kwaskwarima kan yadda rundunar ta ke gudanar da ayyukanta, inda ko a kwanakin baya sai da Shugaban Majalisar Dattawan ƙasar Ahmed Lawan ya ce ba zai yiwu a soke rundunar ba sai dai a sauya tsarinta.
Hakazalika wasu daga cikin ƙusoshin gwamnatin ƙasar da wasu gwamnoni da muƙarraban shugaban ƙasar na da irin wannan ra’ayi.